180804-shendu.m4a
|
Game da wannan batu, kakakin watsa labarai na ma'aikatar kasuwancin kasar Sin ya bayyana cewa, Sin ta dauki matakin ne bisa doka kuma cikin adalci, kana idan ta ga ya zama tilas a dauki mataki, za ta kara daukar wasu matakan da suka wajaba.
Ya ce, Sin ta yi hakan ne domin mayar da martani ga Amurka, wadda ta tsananta batun, da kawo illa ga moriyar kasar Sin da jama'arta, kuma tilas ne a dauki matakai bisa dokokin cinikin kasashen waje da ka'idojin harajin kwastam da ka'idojin dokokin kasa da kasa. Yana mai cewa, ta hakan, za a hana tsananta rikicin cinikin, da tabbatar da moriyar jama'a, da ciniki cikin 'yanci, da tsarin bangarori daban daban da kuma moriyar iri daya na kasa da kasa a duniya baki daya.
Sin ta dauki matakan bisa halin da ake ciki tsakanin Sin da Amurka. Idan kasar Amurka ta kara daukar matakan da ba su dace ba, kamar yadda kakakin ma'aikatar kasuwancin kasar Sin ya bayyana, kasar Sin za ta kara daukar wasu matakai. Sin tana da kasuwa mai girma, da masana'antu a fannoni da dama a duniya, da tsarukan da suka dace, da manufofin bude kofa da sauransu, don haka Sin tana iya fuskantar kalubalen da kasashen waje za su nuna mata. Amma ga kasar Amurka, manufofin bada kariya ga ciniki daga bangare daya da gwamnatin Trump ta dauka sun kawo illa ga kasar, wadanda ake kara kin amincewa da su. Alal misali, a gun taron sauraron ra'ayi da ofishin wakilan kula da ciniki na kasar Amurka da ya gudanar a karshen watan Yuli game da karawa kayayyakin Sin da ake shigar da su Amurka harajin kwastam, mutane 6 cikin masu bada jawabi 82 ne kadai suka amince da kudurin, wadanda adadinsu ya tsaya kan kaso 7 cikin dari kadai. Babu shakka, masu gabatar da manufofi na fadar White Housa ba su samu yawancin goyon baya ba a halin yanzu.
Ga wadannan manyan kasashen masu karfin tattalin arziki a duniya wato Sin da Amurka, ana iya gano wacce ke karfafa tattalin arzikin duniya, da kuma wace ke kawo masa illa. (Zainab)