181204-sharhi-Bello.m4a
|
A ranar 1 ga watan Disamban da muke ciki, shugaban kasar Sin Xi Jinping, da takwaransa na kasar Amurka Donald Trump, sun yi ganawa a kasar Argentina, inda suka yanke shawarar dakatar da matakan takaita ciniki a tsakanin kasashen 2. Sa'an nan kasashen 2 za su kwashe kwanaki 90 suna gudanar da shawarwari, ta yadda za su cimma daidaito wajen soke karin harajin da ake karbar bisa kayayyakin da suke fitarwa. Amma idan an kasa cimma ra'ayi daya, to, kasar Amurka za ta iya ci gaba da aiwatar da yakin ciniki tsakanin kasashen 2.
Game da sakamakon ganawar da shugabannin kasashen Sin da Amurka suka yi, za a iya cewa shugabannin 2 sun taka birki ga takaddamar cinikin da aka samu tsakanin kasashen su, ta yadda suka baiwa al'ummunsu damar yin shawarwari don daidaita sabanin ra'ayi. Sai dai, a sa'i daya, batun ya nuna cewa, tawagogin kasashen 2 za su kaddamar da takara, a watanni 3 masu zuwa, don tabbatar da moriyar kai. Wannan wani aiki ne mai wahala.
Za a iya tambaya cewa, me ya sa kasashen 2 suka iya dakatar da yakin cinikin da ake yi tsakaninsu? Dalilin da ya sa haka shi ne, dukkansu sun sha wahala sakamakon yakin cinikin da suka yi cikin watanni fiye da 8 da suka wuce. Lokacin da aka kaddamar da yakin ciniki a watan Maris na bana, kasar Amurka ta yi tsammanin cewa za ta ci nasara cikin sauki. Amma bayan da aka dinga kara karbar haraji kan kayayyakin da ake fitarwa cikin watanni fiye da 8 da suka wuce, an gano cewa, ba wanda zai iya samun moriya daga yakin cinikin. Wasu alkaluman da aka samu sun shaida cewa, gibin cinikin da kasar Amurka ta samu a watan Oktoban bana ya kai dalar Amurka biliyan 77.2, wanda ba a taba ganin yawansa ya kai haka ba a tarihin kasar. Haka zalika, a karshen watan Nuwanba, kamfanin samar da motoci na GM na kasar Amurka, ya sanar da rufe ma'aikatunsa guda 7 dake kasashe daban daban, ciki har da wasu 4 dake cikin gidan kasar Amurka, lamarin da ya haifar da matsin lamba sosai ga gwamnatin kasar Amurka. Ban da haka kuma, jarin waje da kasar Amurka ta janyowa kanta tsakanin watan Afrilu da na Yunin bana ya ragu sosai, har zuwa wani matsayin da ba a taba ganinsa ba tun daga shekarar 2015. Wadannan abubuwa sun shaida cewa, yakin cinikin da kasar Amurka ta tayar bai taimaka mata wajen biyan bukatunta na rage gibin ciniki, samar da karin guraben ayyukan yi a gida, da janyo karin jarin waje ba, maimakon haka ya kara hadarin da take fuskanta a fannin tattalin arziki. Ta la'akarin da wannan yanayin da ake ciki, ko kasar Amurka za ta iya ci gaba da yakin ciniki? Saboda haka, lokacin da shugaba Donald Trump ke hira da wakilin kafar watsa labarai ta CBS a ranar 14 ga watan Oktoba, ya ce wani "karamin rikici" maimakon "yakin ciniki" ne aka samu tsakanin kasashen Sin da Amurka, kana yana kokarin neman saukaka wannan rikici.
Yanzu shugabannin kasashen Sin da Amurka sun taka birki ga takaddamar ciniki, lamarin da zai amfani dukkan bangarorin 2. Daga bisani, idan tawagogin kasashen 2 za su iya cimma matsaya a shawarwarin da za su gudanar, to, hakan zai zama alheri ga kowa. Amma idan an kasa samun masalaha tsakaninsu, to, watakila za su sake kaddamar da yakin ciniki, lamarin da zai haifar da wani yanayi na rashin tabbas ga kasashen 2, gami da duniyarmu baki daya.
Sai dai wa'adi na watanni 3 da aka kayyade zai ba tawagogin 2 wahala, domin abubuwan da za su tattauna na da sarkakiya. Game da bukatu na bangaren Amurka, manufar kasar Sin ita ce, za a tattauna su, matukar ba su sabawa manufar kasar ta bude kofa ga kasashen waje da gyare-gyare a cikin gida ba. Sa'an nan kasar Amurka ita ma ta mayar da martani ga wasu bukatun da kasar Sin ta gabatar. Sai dai yayin da aka fara shawarwarin, tabbas ne, bangarorin 2 za su yi takara mai tsanani a tsakaninsu. Kuma akwai yiwuwar gamuwa da wuya wajen samun daidaito a tsakaninsu. Amma bangaren kasar Sin ya nuna wani yanayi na rashin tsoro dangane da duk wani sakamakon da za a iya samu. Da ma ba wai kasar Sin ce ta kaddamar da yakin ciniki a wannan karo ba, tana mayar da martani ne ga matakan kasar Amurka kawai. Ra'ayin kasar Sin shi ne: ba ta son yakin ciniki, kuma ba ta tsoronsa. Idan ya wajaba, to, kasar za ta yi yakin ciniki don tabbatar da moriyarta da ta jama'arta. Hakika shawarwarin da bangaren Sin ta yi da Amurka a baya, ya riga ya shaida karfin zuciya da imanin da kasar ke da su. (Bello Wang)