in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sojojin Amurka sun kashe mayakan al-Shabab 2 a Somaliya
2019-02-25 10:20:32 cri

Dakarun sojojin Amurka sun sanar a jiya cewa, sun hallaka mayakan 'yan ta'adda na al-Shabab biyu a wasu hare-hare hudu da suka kaddamar ta sama a kudancin kasar Somaliya, a ranar Asabar.

An kai hare-haren ta sama hudu ne a lokuta daban daban a yankunan Kunyow Barrow, Awdeegle, da Janaale, inda suka tarwatsa wasu shingayen binciken ababen hawa da mayakan na al-Shabab ke amfani da su, kwamandan rundunar dakarun Amurka dake Afrika wato (AFRICOM) ya sanar da hakan.

Bisa sanarwar, an ce, babu wani farar hula da aka jikkata ko aka kashe a lokacin kai hare-haren ta sama.

AFRICOM ta ce hare-haren ta sama suna matukar tallafawa dakarun kasar Somaliya wajen samun galaba kan mayakan al-Shabab, kuma wani bangare ne na kokarin da suke yi wajen baiwa al'ummar kasar Somaliya kariya daga ayyukan ta'addanci.

Sanarwar ta kuma nuna cewa, jami'an tsaron kasar Somaliya suna ci gaba da kokarin murkushe mayakan na al-Shabab domin tabbatar da fadada ikon da gwamnatin kasar Somaliyan ke da shi.(Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China