Rahoton nazarin bayan yanayin Deyr da hukumar kula da samar da abinci da harkokin gona na MDD da sashen kula da wadatuwar abinci da nazarin abinci mai gina jiki na Somalia ke kula da shi, da shirye-shiryen gargadin wuri kan aukuwar yunwa suka fitar, ya ce akwai yiwuwar wasu yara 903,100 'yan kasa da shekaru 5 su fuskanci matsananciyar tamowa a bana.
Yanayi a kasar Somalia ya hada da Xagaa wanda ke farawa daga watan Yuli zuwa Satumba da Deyr dake farawa daga Oktoba zuwa Disamba, sai yanayin Jilal daga Disamba zuwa Maris da kuma Gu dake farawa daga karshen watan Maris zuwa na Yuni.
Rahoton ya ce ruwan sama na lokacin Deyr ya yi jinkirin sauka, kuma bayan saukarsa, bai kai matsakaicin mataki ba a galibin yankunan kasar, inda sassa mai yawa na tsakiyar kasar da wasu sassa na arewaci suka samu kasa da kaso 25 zuwa 50 na matsakaicin ruwan saman. Haka kuma, ba a samu wani rahoton ambaliya ba.
Rahoton ya kuma kara da cewa, ya zuwa watan Janairu, dorewa da fadadar ayyukan agaji sun hana yanayin rashin abinci ta'azzara a yankuna da dama na kasar. (Fa'iza Mustapha)