Rundunar wadda ta bayyana hakan a jiya Asabar cikin wata sanarwa, ta ce ta kaddamar da harin ne a ranar Juma'a, kuma babu wani farar hula da ya rasu, ko ya jikkata sakamakon harin.
AFRICOM ta kara da cewa, a baya mayakan Al-Shabab din sun yi amfani da yankin Gandarshe, mai nisan kilomita 48 daga kudu maso yammacin birnin Mogadishu, fadar mulkin kasar, domin kaddamar da hare-hare da ababen fashewa, ta amfani da ababen hawa kan mazauna babban birnin kasar.
A ranar 15 da 16 ga watan Disambar da ya shude ma, sojojin Amurkan sun kaddamar da hare-hare ta sama guda shida, wadanda suka hallaka mayakan mungiyar 62, a wani wuri dake kusa da Gandarshe, wurin da a cewar tawagar ta AFRICOM, Al-Shabab ta shirya amfani da shi wajen kaiwa sansanin sojojin gwamnatin Somalia dake wurin hari.
Har ila yau a Larabar da ta gabata ma, wani harin ta sama da sojojin suka kaddamar, ya yi sanadin hallaka mayakan kungiyar 24 a yankin Hiran mai makwaftaka da Gandarshe. (Ahmad Fagam)