in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Somaliya da MDD sun lashi takobin karfafa dangantakarsu dangane da aiwatar da sauye sauye
2019-01-31 10:24:48 cri

Kasar Somaliya da MDD, sun kuduri niyyar karfafa dangantakarsu dake da nufin aiwatar da sauye-sauye a kasar dake kahon Afrika.

Shugaban Somalia Abdullahi Farmajo, wanda ya tattauna da mataimakiyar Sakatare Janar na MDD kan harkokin siyasa da wanzar da zaman lafiya, Rosemary DiCarlo a birnin Mogadishu, ya yi alkawarin aiki kafada da kafada da majalisar, domin taimakawa ginawa da wanzar da zaman lafiya a kasar.

Wata sanarwar hadin gwiwa da suka fitar, ta ce Gwamnatin Somalia da MDD, na sa ran zurfafa dadaddiyar dangantakarsu, domin ba Somalia damar ci gaba da samun nasara wajen samun zaman lafiya mai dorewa.

Sanarwar ta ruwaito Rosemary Dicarlo, wadda ta isa birnin Mogadishu a jiyan, ta tattauna sosai da shugaban kasar, tare da bayyana kudurin fadada dangantakar dake tsakanin Gwamnatin Somalia da MDD.

Yayin taron wanda ya samu halartar Firaministan Somalia, Hassan Ali Khaire, shugabannin 3 sun tattauna kan kwararan hanyoyin da gwamnatin da MDD za su bi wajen aiki da juna domin amfanawa al'ummar Somalia. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China