A wannan rana da safe kuma, ofishin kwamandan sojojin Amurka dake Afirka ya sanar da cewa, a ranar 8 ga wata, sojojin Amurka sun dauki matakin kai hari ta sama ga sansanin kungiyar Al-Shabab dake kusa da garin Kismayo, inda ake da tashar teku dake kudancin kasar Somaliya, amma bai sanar da adadin mutanen da suka mutu ko suka ji rauni a sakamakon wannan harin ta sama ba.
Kungiyar Al-Shabab, wata kungiyar masu tsattsaurar ra'ayi ce dake da alaka da kungiyar Al-Qaeda. A 'yan shekarun baya bayan nan, ta sha kai hare-haren ta'addanci a kasar Somaliya ko sauran kasashe wadanda suke makwabtaka da kasar ta Somaliya. (Sanusi Chen)