in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An mayar da bakin haure 116 daga gabashin Libya zuwa Najeriya wadanda suka nemi komawa gida da kansu
2019-01-31 10:54:39 cri
Hukumar kula da makaurata ta kasa da kasa (IOM) a jiya Laraba ta sanar da cewa ta kwashe bakin haure 116 wadanda suka nemi komawa gida da kansu daga gabashin Libya zuwa Najeriya.

A cewar ofishin yada labarai na ma'aikatar cikin gidan kasar dake gabashin Libya, an gudanar da aikin mayar da bakin hauren ne daga birnin Benghazi dake gabashin kasar zuwa Najeriya.

Wannan shi ne aikin kwashe bakin haure wadanda suka nemi komawa gida da kansu irinsa na farko daga gabashin Libya, tun bayan da hukumar IOM ta fara gudanar da aikinta daga yammacin Libyan, inda ake samun bakin haure masu yawa dake neman tsallakawa Turai ta Bahar Rum.

"An kwashe bakin hauren daga filin jirgin saman kasa da kasa na Benina zuwa Benghazi, bayan an biya musu dukkan bukatunsu," inji ma'aikatar.

Libya tana fama da rikicin shugabanci tsakanin gwamnatin gabashi da yammacin kasar, inda kowane bangare yake ikirarin kasancewa halastacciyar gwamnati.

Hukumar IOM tana gudanar da shirin mayar da bakin haure zuwa kasashensu na asali wadanda ke gararamba a kasar Libya. Ya zuwa shekarar 2018, IOM ta kwashe bakin hauren da suka nemi komawa gida da kansu kimanin 16,000 daga kasar ta Libya zuwa kasashensu na asali.(Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China