in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sojojin ruwan Libya sun ceto bakin haure 113 a gabar ruwan yammacin kasar
2018-11-26 10:42:11 cri
Rahotanni daga kasar Libya na cewa, sojojin ruwan kasar sun yi nasarar ceto bakin haure da suka hada da mata da yara kanana da yawansu ya kai 113 a gabar ruwan yammacin kasar, kilomita 75 daga Tripoli, babban birnin kasar

Wata sanarwar da rundunar sojojin ruwan kasar ta fitar, ta bayyana cewa, masu tsaron gabar teku tare da hadin gwiwar wani jirgin ruwa mallakar wani kamfanin hakar gas ne suka ceto bakin haure a cikin wani kwale-kwalen roba. Galibin bakin hauren dai sun fito ne daga kasashen Afirka.

Sanarwar ta ce, an garzaya da bakin haure da aka ceto zuwa wata cibiya dake kusa da garin Zawiya, kimanin kilomita 45 yamma da birnin Tripoli.

Dubban bakin haure ne dai ke kokarin ketare tekun Bahar-Rum don neman shiga Turai daga kasar ta Libya, sakamakon rashin tsaron da kasar ke fama da shi biyo bayan boren shekarar 2011. (Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China