IOM wanda ta gudanar da aikin sa kai karkashinn shirin mayar da bakin haure kasashensu na asali tare da hadin gwiwar hukumomin kasar Libyan, da nufin mayar da bakin hauren wadanda ke gararamba a kasar ta Libya.
Kasar Libya ta zama tamkar wata cibiyar da bakin haure ke ribibin zuwa da nufin tsallakawa kasashen Turai ta tekun Mediterranean sakamakon matsalar tabarbarewar tsaro da tashin hankalin da kasar ta arewacin Afrika ta tsunduma tun bayan kifar da gwamnatin tsohon shugaban kasar Muammar Gaddafi a shekarar 2011. (Ahmad Fagam)