in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
MDD: 'Yan ci rani na shiga mummunan hali a Libya
2018-12-21 10:20:02 cri

Wani rahoto na tawagar wanzar da zaman lafiya a Libya ko UNSMIL a takaice, ya ce 'yan ci rani dake shiga kasar Libya da nufin tsallakawa sassan nahiyar Turai ta tekun Meditereniya, na fuskantar mawuyacin hali na cin zarafi ko ma kisa.

Rahoton wanda aka fitar a jiya Alhamis, na kunshe da alkaluman kididdigar na watanni 20, tun daga bara ya zuwa watan Agustan shekarar nan ta 2018.

Kaza lika rahoton ya zargi wasu jami'an hukuma, da masu dauke da makamai, da masu fasa kwauri, da aikata laufukan da suka hada da cin zarafin 'yan ci rani da bakin hauren, inda a wasu lokuta ake tilasa musu yin ayyukan bauta, ko yin lalata da su. A wani sa'in ma rahoton ya ce ana tsare bakin hauren, ko a yi musu fashi, baya ga wasu da dama da ake hallakawa.

Da yake tsokaci game da hakan, babban kwamishinan MDD mai lura da kare hakkokin bil Adama Michelle Bachelet, ta yi kira ga masu ruwa da tsaki, da su gaggauta daukar matakan dakila wadannan matsaloli dake addabar dubban 'yan gudun hijira da'yan ci rani, da suka hada da mata da kananan yara, masu neman mafaka da kyakkyawar rayuwa.(Saminu Alhassan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China