190222-an-shaida-sabuwar-alama-a-cikin-takardar-dake-shafar-aikin-noma-da-kauyuka-manoma-ta-sin.m4a
|
A ranar 19 ga wannan wata, Sin ta gabatar da takardar manufofi ta farko ta shekara bana kan yadda za a raya aikin noma da kauyuka da manoma, wannan ne takardar dake shafar aikin noma da kauyuka da manoma da Sin ta sa lura da ita har na tsawon shekaru 16 a jere. Bisa sabon yanayin da Sin take ciki na canjawa zuwa samun bunkasuwar tattalin arzikin kasar mai inganci da kuma karuwar bukatun jama'ar kasar, takardar ta shaida sabuwar alama ta yin kwaskwarima a gida da bude kofa ga kasashen waje. Wannan ya shaida cewa, manyan shugabannin kwamitin tsakiya na jam'iyyar kwaminis ta Sin suna lura sosai ga batun aikin noma da kauyuka da manoma, kuma tilas ne a warware matsalolinsu yayin da Sin take shiga muhimmin lokacin raya zamantakewar al'umma mai wadata.
Tsaron hatsi tushe ne na batun aikin noma da kauyuka da manoma na kasar Sin. A halin yanzu, fadin filayen aikin goma na kasar Sin ya kai kashi 10 cikin dari bisa na duniya, wanda ya ciyar da yawan mutane da kashi 20 cikin dari na duniya, don hakan tsaron hatsi ya zama mafi muhimmanci. Game da wannan batu, takardar ta jaddada inganta tsaron hatsi da kuma yin kwaskwarima kan tsarin samar da amfanin gona bisa bukatu.
"Ba za a damu ba idan akwai isassun abinci a hannu", wannan ne fasahar da Sin ta samu a tarihi, shi ne kuma ra'ayin bai daya da Sinawa suka samu a cikin shekaru 40 da aka gudanar da manufar yin gyare-gyare a cikin gida da bude kofa ga kasashen ketare. Sau da yawa shugaban kasar Sin Xi Jinping ya jaddada cewa, dole ne Sinawa su kiyaye kwanonsu. To yaya za a kiyaye kwanon? A cikin takardar, an gabatar cewa, kamata ya yi a bada tabbaci ga shuka hatsi na muraba'in hekta miliyan 110, da fadin gonaki da ya kai a kalla hekta miliyan 120, da fadin gonaki mai dorewa a kalla hekta miliyan 100, kana ya zuwa shekarar 2020 za a kafa gonaki masu inganci sama da hekta miliyan 53. Baya ga haka, za a maida shinkafa da alkalma a matsayin muhimman hatsi don tabbatar da isassun abinci, da bada tabbaci ga samar da masara, da kara gaggauta yunkurin kafa dokokin tabbatar da isassun abinci da dai sauransu. Dukkansu sun nuna niyya da karfin gudanarwa na kasar Sin wajen tabbatar da samun isassun abinci da cimma burin kawar da talauci a matsayinta na wata babbar kasa a fannin aikin gona da kasa mai tasowa mafi girma a duniya.
A daya bangaren kuma, saboda yadda Sinawa suke bukatar karin amfanin gona masu inganci, babbar matsalar da kasar Sin ke fuskantar a fannin aikin gona ta riga ta canza daga "babu isashen amfanin gona" zuwa "rashin daidaituwa tsakanin abin da ake samarwa da abin da ake bukata". A wajen taron baje kolin kayayyakin da ake shigowa da su kasar Sin irinsa na farko da ya gudana a birnin Shanghai na kasar Sin a bara, kayayyakin da kamfanoni fiye da 1000 daga kasashe fiye da 100 suka zo da su sun samu karbuwa sosai a kasuwar kasar Sin. Don biyan bukatun jama'ar kasar Sin kimanin biliyan 1.4 a fannin abinci, takardar ta bana ita ma ta tanada cewa, ya kamata a kara shigo da amfanin gona wadanda ba a samu isashensu ba a nan kasar Sin, gami da kara hanyoyin da ake bi wajen shigo da amfanin gonan. A nan ya kamata mu lura da abubuwa guda 2 masu muhimmanci, daya shi ne dalilin da ya sa za a kara shigo da amfanin gona shi ne domin biyan bukatun jama'ar kasar. Sa'an nan batu na 2 shi ne, za a kara hanyoyin da ake bi wajen shigo da kayan. Hakan na nufin, kasar Sin tana neman hadin gwiwa da kasashe daban daban. Za a shigo da duk wani irin amfanin gona, matukar dai yana da inganci da araha, kuma yana samun karbuwa a kasuwar kasar Sin.
A matsayinta na kasa mafi girma wajen bukatar kayayyakin aikin gona a fadin duniya, kasar Sin ta kara shigo da kayayyakin aikin gonar da take da karancin su daga kasashen ketare, ta yadda za ta samar da isassun kayayyakin ga al'ummar kasar, misali ga wake, yanzu adadin naman da Sinawa suke ci a cikin shekarun baya bayan nan ya karu cikin sauri, amma ana fama da karancin wake yayin da ake kiwon dabbobi, shi ya sa kasar Sin tana shigo da wake daga kasashen ketare kamar su Amurka, saboda kasashen suna sayar da wake ne da farashi mai araha, kana ana iya tace man girki daga waken, haka kuma ana iya samar da abinci ga dabbobin da ake kiwo.
Haka zalika kara shigo da kayayyakin aikin gona daga kasashen ketare zai taimaka wajen kyautata tsarin kayayyakin aikin gona a kasuwar kasar Sin, kan batun, takardar ta yi nuni da cewa, ya kamata a kara kyautata tsarin aikin gona tare kuma da kara samar da kayayyakin aikin gona masu inganci, kana ya dace a aiwatar da shirin raya aikin samar da wake da abincin da ake samarwa da madara da sauransu. A sa'i daya kuma, ya kamata a sanya kokarin amfani da sabuwar fasahar gudanar da aikin gona, tare da horas da kwararru wadanda suke da tunanin kirkire-kirkiren kimiyya da fasaha kan aikin gona, da haka za a ingiza ci gaban aikin gona daga dukkan fannoni a kasar ta Sin yadda ya kamata.
A hakika, wadannan su ne manufofin ayyukan gonar da gwamnatin kasar Sin ke aiwatarwa, har ma sun bayyanawa kasashen duniya manyan batutuwan da kasar ke maida hankali a bangaren aikin gona. Tabbas, wadannan bangarori za su kasance muhimman bangarorin da kasar Sin za ta hada kai tare da kasashen ketare a fannin aikin gona. A yayin da kasar Sin ke kokarin bude kofarta ga kasashen waje da yin gyare-gyare a cikin gida, ayyukan gonar kasar za su kara karfin yin takara a duniya, kana Sin za ta kara samar da isasshen abinci ga al'ummarta, ta yadda kasar za ta iya tinkarar duk wani kalubale da hadarin da take fuskanta, da cimma burin neman bunkasuwar tattalin arziki da zamantakewar al'umma cikin lokaci.(Masu fassara:Zainab,Bilkisu,Bello,Jamila,Murtala)