Mista Geng ya ce, Sin babbar kasa ce dake sayo amfanin gona daga Amurka. A shekaru da dama, hadin-gwiwar Sin da Amurka a fannin ayyukan gona ya habaka ya kuma inganta, wanda hakan ya haifar da babbar moriya ga bangarorin biyu.
Irin wannan mawuyacin hali da ake ciki, ya samo asali ne sakamakon matakan bada kariya ga harkokin cinikayya da Amurka ta dauka, gami da rashin cika alkawarin da ta dauka, har ta kaddamar da yakin cinikayya da gangan kan kasar Sin.
Kasar Sin na fatan gwamnatin Amurka za ta saurari ra'ayoyi daga bangarori daban-daban na kasarta, za ta kuma saurari ra'ayoyi daga kasashen duniya daban-daban, da kara fahimtar halin da ake ciki yanzu, bai kamata kuma ta ci gaba da aikata laifi a wannan fanni ba.(Murtala Zhang)