Tun a shekarar 2011, Kasar Sin ta fara kokarin samar da gonar da zata iya jure ambaliya da fari, a wani yunkuri na tabbatar da wadatar abinci. Ya zuwa karshen shekarar 2018, kasar ta samar da gonar da fadinta ya kai kadada kusan miliyan 43, inda kowane mu, zata rika samar da nau'in amfanin gona da ya kai kilogram100.
A cewar Zhang Xiaoshan, malami a kwalejin nazarin kimiyyar zamantakewa ta kasar Sin, Samar da ingantattun gonakin noma da manyan injinun aikin gona da ingantattun tsirrai mabanbanta, za su taimakawa kasar Sin tabbatar da samun wani matsayi mai dinbin alfanu a kasuwar amfanin gona ta duniya. (Fa'iza Mustapha)