Shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya baiwa daukacin sassan dake da alhakin aiwatar da shirye-shiryen raya yankunan karkara, umarnin kara zage damtse wajen sauke nauyin dake kan su yadda ya kamata.
Shugaba Xi wanda shi ne babban sakataren kwamitin koli na JKS, kana jagoran hukumar zartaswar rundunar sojin kasar, ya ce raya yankunan karkara shi ne jigon inganta sha'anin noma, da kyautata rayuwar mazauna yankunan a sabon zamanin da ake ciki.
Cikin umarnin na Shugaba Xi, ya ce kamata ya yi ayyukan da za a gudanar, su shafi fannonin raya masana'antu, da bunkasa basirar al'umma, da raya al'adu, da inganta muhalli, da kyautata tsarin yankunan karkara.
Ya ce bisa wannan kuduri, ya dace a karfafa gwiwar mazauna yankunan karkara, a kuma zaburar da kwazon al'umma, ta yadda kowa zai samu kuzarin cimma nasara, da samun farin cikin nasarorin da za a mora, da kuma bunkasa tsaro.(Saminu Alhassan)