Shawarwarin sun ce, bara da bana, muhimman lokaci ne wajen raya zaman al'umma mai matsakaicin karfi daga dukkan fannoni a kasar Sin, kuma a bangarorin sana'ar noma da karkara gami da manoma, akwai jan aiki a gaba. Kwamitin tsakiya na jam'iyyar Kwaminis ta kasar Sin na ganin cewa, yayin da kasar Sin ke fuskantar matsin bunkasar tattalin arziki da sauye-sauyen yanayin duniya da ake ciki, bunkasa harkoki a wadannan bangarorin uku, wato noma da karkara gami da manoma, na da muhimmanci matuka. Har wa yau, kamata ya yi jam'iyyar Kwaminis mai rike da ragamar mulki a kasar ta tsaya tsayin daka wajen gudanar da ayyuka a wadannan fannoni uku.
Shawarwarin sun ce, ya zama dole a yi azama wajen kawar da fatara a duk fadin kasar Sin, don neman cimma burin yaki da talauci a yankunan karkara, karkashin mizanin da kasar ke amfani da shi yanzu ya zuwa shekara ta 2020.
Bugu da kari, shawarwarin sun ce, ya kamata a inganta tushen sana'ar noma, da tabbatar da samar da isasshen amfanin gona, tare kuma da kyautata tsarin ayyukan gona, da nazarin kimiyya da fasaha a bangaren noma.(Murtala Zhang)