Taron, wanda aka gudanar a birnin Alkahira, ya tabo al'amurran da suka shafi rawar da hukumomin shari'a za su taka wajen yaki da rashawa da kare hakkin bil'adama, kakakin fadar shugaban kasar Masar Bassam Rady shi ne ya bayyana hakan.
Taron dai ya zo ne jim kadan bayan da kasar Masar ta karbi jagorancin kungiyar tarayyar Afrika a farkon wannan wata.
Sisi ya jaddada muhimmancin karfafa rawar da dokoki da bangaren shari'a za su taka a kasashen Afrika, wanda rashin kyautata su ke haifar da matsaloli kamar na ayyukan ta'addanci da tsattsauran ra'ayi.
Shugaban kasar Masar ya bayyana ta'addanci da cewa shi ne babban kalubale dake addabar duniya baki daya.(Ahmad Fagam)