in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Masar ta karbi bakuncin taron albarkatun mai na kasa da kasa
2019-02-12 15:21:08 cri
Firaministan kasar Masar Mostafa Madbouly, a jiya Litinin ya kaddamar da taron kasa da kasa kan albarkatun man fetur a birnin Alkahira.

A jawabinsa na bude taron, Madbouly ya ce taron zai samar da damammaki wanda zai amfanawa ko wane bangare.

Haka zalika ya jaddada aniyar kasar Masar na cigaba da bullo da shirye-shiryen da za su taimaka wajen bunkasar tattalin arzikin kasar a shekarun baya bayan nan.

Take taron shi ne "Shiyyar arewacin Afrika da Bahar Rum: Cimma nasarar bukatun da ake da su na makamashi a nan gaba," taron wanda aka gudanar karkashin ikon shugaban kasar Masar Abdel-Fattah al-Sisi, kuma ana sa ran halartar jami'ai daga yankin kasashen Larabawa da ministocin albarkatun mai na kasashen Afrika.

Taron zai mayar da hankali ne kan batutuwan tsaron makamashi, da lafiyar mata, da tsaro, da kare muhalli, da kuma harkokin kudi da zuba jari, inda sama da wakilai 200 za su gabatar da jawabai, ciki har da jami'an kula da masana'antu da kwararru, da kuma wakilai 1,200.(Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China