A lokacin bikin kaddamarwar, shugaban jami'ar Ain Shams, Abdel Wahab Ezzat ya ce, an kafa cibiyar ne bayan wata yarjejeniyar da aka cimma cikin shekara guda, wanda daga bisani aka kulla yarjejeniyar fahimtar juna wanda jami'ar ta rattaba hannu, yayin da Liu Wei, shugaban jami'ar Renmin ta kasar Sin ya sanya hannu a madadin jami'arsa.
"Wannan ita ce cibiya ta biyu bayan makamanciyarta ta farko da aka kafa a kasar Rasha," in ji shi, ya kara da cewa, cibiyar za ta gudanar da nazari kan sha'anin tattalin arziki, kasuwanci da nazarin samar da kwararru, game da ayyukan hadin gwiwa tsakanin kasashen Masar da Sin.
A nasa bangaren, Liu Wei ya yaba da kafa cibiyar hadin gwiwar da jami'ar ta Ain Shams. (Ahmad Fagam)