in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Yang Jiechi ya gana da shugaban kasar Masar
2019-01-17 10:37:42 cri
Wakilin musamman na shugaban kasar Sin Xi Jinping kuma memban hukumar siyasa ta kwamitin tsakiyar jam'iyyar kwaminis ta Sin kuma shugaban ofishin kula da harkokin waje na kwamitin tsakiyar Yang Jiechi ya gana da shugaban kasar Masar Abdel-Fattah al-Sisi a birnin Alkahira.

Yang Jiechi ya yi nuni da cewa, a cikin jawaban da shugaba Xi Jinping ya yi a shekarar bara a gun bikin bude taron koli na Beijing na dandalin tattaunawa kan hadin gwiwar dake tsakanin Sin da Afirka da kuma bikin bude taron ministoci karo na 8 na dandalin hadin gwiwa a tsakanin Sin da kasashen Larabawa, ya gabatar da sabbin matakan raya hadin gwiwar dake tsakanin Sin da Afirka da kuma kasashen Larabawa. Kasar Masar babbar kasa ce ta yankin Larabawa da ta nahiyar Afirka, kana za ta zama kasar shugaba ta karba karba ta kungiyar AU. Kasar Sin tana son kara yin hadin gwiwa tare da kasar Masar wajen aiwatar da ayyukan da aka cimma daidaito da sa kaimi ga raya hadin gwiwar dake tsakanin Sin da Afirka da kasashen Larabawa zuwa wani sabon matsayi.

A nasa bangare, shugaba al-Sisi ya bukaci Yang Jiechi da isar da gaisuwa ga shugaba Xi Jinping. Al-Sisi ya bayyana cewa, ana sada zumunta a tsakanin Masar da Sin, kasar Masar ta nuna yabo ga fasahohin bunkasuwa da kasar Sin ta samu, da maida hankali ga matsayin kasar Sin a duniya. Kana Masar tana son ci gaba da aiwatar da ayyukan da shugabannin kasashen biyu suka cimma daidaito da kuma sa kaimi ga raya shawarar "ziri daya da hanya daya". (Zainab)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China