in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Masar ta kara wa'adin dokar ta baci da watanni 3
2019-01-14 09:46:56 cri
A jiya Lahadi ne majalissar dokokin kasar Masar, ta amince da kara wa'adin dokar ta baci a wasu yankunan kasar da watanni 3. Matakin dai ya biyo bayan matsalolin tsaro ne da aka fuskanta a lardunan kasar na Gharbiya da Alexandria.

Kamfanin dallancin labarai na MENA ya bayyana cewa, majalissar ta amince da kudurin doka da shugaban kasar ta Masar Abdel-Fattah al-Sisi ya gabatar, wadda a sabon zagayen wa'adin ta, za ta fara aiki tun daga ranar 15 ga watan nan na Janairu.

Karkashin tanajin dokar, sojoji da 'yan sanda za su iya daukar dukkanin wani mataki na yaki da 'yan ta'adda, tare da tabbatar da tsaro a daukacin sassan kasar.

Shugaba Abdel-Fattah al-Sisi ya kaddamar da dokar ta bacin a karon farko ne a watan Afirilun shekarar 2017, biyowa bayan tagwayen bama bamai da suka fashe a lardunan Gharbiya da Alexandria dake arewacin kasar, lamarin da ya hallaka mutane a kalla 47, tare da raunata wasu 120. (Saminu Hassan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China