Labarin ya bayyana cewa, wannan mutum dan shekaru 18 da haihuwa, 'yan sanda sun kama shi bayan da ya sauka daga jirgin sama daga kasar Jamus zuwa filin jiragen sama na Luxor dake kudancin kasar Masar a kwanakin baya, kuma a ranar 13 ga wata, aka kore shi daga kasar Masar.
Labarin ya bayyana cewa, 'yan sanda sun gano taswirar arewacin zirin Sinai na kasar Masar da kungiyar IS ta kan gudanar da ayyuka a jikin wannan mutum, kuma wannan mutum ya amince da yunkurinsa na shiga kungiyar IS.
Labarin ya kara da cewa, an haifi wannan mutum a kasar Masar, bayan da ya zama dan kasar Jamus, ya yi watsi da zama dan kasar Masar a shekarar 2007.
A ranar 11 ga wannan wata, gwamnatin kasar Masar ta kori wani dan kasar Jamus da aka zarga da yunkurin shiga kungiyar IS. (Zainab)