in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
AU da MDD: an samu nasarori bisa aiwatar da yarjejeniyar zaman lafiya a Sudan ta Kudu
2018-10-10 09:44:45 cri
Manyan jami'an MDD da Tarayyar Afrika (AU), sun ce akwai raguwar rikice-rikice a Sudan ta Kudu idan aka kwatanta da bara, biyo bayan yarjejeniyar zaman lafiya da bangarori masu adawa da juna suka sanyawa hannu a karshen watan Augustan da ya gabata.

Yayin da yake kammala ziyarar yini 3 a Sudan ta Kudu a jiya, Mataimakin Sakatare Janar na MDD kan ayyukan wanzar da zaman lafiya Jean Pierre Lacroix, ya bayyanawa manema labarai a Juba cewa, sun samu kwarin gwiwa saboda ci gaban da aka samu daga bangarorin masu rikici, musammam na tsagaita bude wuta yayin da rikici ya barke a bayan- bayan nan a kudu maso yammacin jihar Yei River da jihar Unity

Ita kuwa babbar daraktar hukumar kula da harkokin mata ta MDD Phumzile Mlambo-Ngcuka, cewa ta yi, matan Sudan ta Kudu na son a yi aiki da su a fannin sake fasalin tsarin tsaro, wanda ya kunshi ba su dama ta taka rawa tare da bada gudunmuwa wajen tabbatar da tsaron kasar wanda zai haifar da raguwar ayyukan soji.

A nasa bangaren, Smail Chergui na kwamitin tsaro na AU, ya ce kowa da kowa musammam ma fararen hula, na kara fata da bukatar aiwatar da yarjejeniyar da aka cimma tsakanin shugaban kasar Salva Kiir da shugaban 'yan tawaye Riek Machar da sauran bangarori 'yan adawa. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China