in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Asusun UNICEF ya bayyana muhimman matakan kare yara a Jamhuriyar Afrika ta tsakiya
2019-02-19 10:49:24 cri
Asusun kula da kananan yara na MDD UNICEF, ya zayyana wasu matakan kare yara da ya kamata a dauka a Jamhuriyar Afrika ta Tsakiya CAR.

Da yake yabawa yarjejeniyar zaman lafiya da bangarori 15 masu rikici suka sanyawa hannu a CAR, asusun UNICEF ya ce yanzu ne lokacin da ya kamata a yunkura, tare da fitar da matakan da ya kamata kungiyoyi masu dauke da makamai da hukumomin shari'a da gwamnati su dauka don kare makomar miliyoyin yara.

Cikin wata sanarwa da ta fitar, babbar daraktar UNICEF Henrietta Fore, ta ce yarjejeniyar da aka cimma tsakanin gwamnatin kasar da sauran kungiyoyi masu rikici, matakin farko ne na cimma zaman lafiya da fatan samun kyakkyawar makoma ga yaran kasar.

Tun bayan da rikici ya barke a kasar cikin shekarar 2012, tsakanin 'yan kungiyar anti-Balaka da galibinsu kirista ne da kungiyar 'yan tawaye ta Seleka, galibi musulmai, dubban fararen hula ne suka mutu yayin da 2 cikin mutane 3 a kasar ke dogaro da agajin jin kai.

A cewar asusun, rikicin ya fi shafar yara, inda 1 cikin yara 4 ke rashin matsuguni a kasar da ba ta da iyaka da teku, ko kuma kasashe makwabta, yayin da har yanzu akwai miliyoyinsu da ba sa zuwa makaranta da fama da tamowa da cututtuka da cin zarafi da bauta. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China