Shugaba Xi ya yi nuni da cewa, dangantakar dake tsakanin Sin da Amurka, tana daya daga cikin muhimman alakokin kasa da kasa a duk fadin duniya. Kuma raya dangantakar kasashen biyu ta dace da muhimman muradun jama'arsu baki daya. Xi ya ce, a watan Disambar bara, shi da takwaransa na Amurka Donald Trump sun yi shawarwari a kasar Argentina, inda suka bayyana fatan cewa, tawagogin kasashen biyu za su himmatu wajen daidaita sabanin ra'ayin dake tsakaninsu da ciyar da hadin-gwiwarsu ta fannin tattalin arziki da kasuwanci gaba.
Xi ya kara da cewa, daga watan Disambar bara, zuwa yanzu, tawagogin ma'aikatan tattalin arziki da kasuwanci na kasashen biyu sun gudanar da shawarwari masu muhimmanci tsakaninsu. Kuma Sin na fatan za su daidaita sabaninsu ta hanyar yin hadin-gwiwa, da kokarin cimma yarjejeniyar da dukkan bangarorin biyu za su amince da ita. Xi ya ce, a wadannan kwanaki, an cimma wasu muhimman nasarori a yayin shawarwarin tawagogin na Sin da Amurka, kana, a makon gobe, bangarorin biyu za su sake ganawa da juna a birnin Washington na kasar Amurka, kuma ana fatan za su yi kokarin cimma yarjejeniyar hadin-gwiwa da za ta amfani juna
A nasu bangaren, Robert Lighthizer da Steven Mnuchin sun bayyana cewa, dangantakar Sin da Amurka ta fannin kasuwanci na da matukar muhimmanci. Kuma a cikin wadannan kwanaki, bangarorin biyu sun gudanar da muhimmiyar tattaunawa kan batutuwan tattalin arziki da kasuwanci dake jawo hankulansu dukka, da samun sabbin ci gaba a wasu fannoni da dama. A nan gaba kuma, tawagar Amurka za ta yi kokarin aiki tare da tawagar kasar Sin don cimma yarjejeniyar kawowa juna moriya.(Murtala Zhang)