Cikin sakonsa, shugaba Xi Jinping na kasar Sin, ya bayyana fatansa na ganin kasashen Sin da Sudan su karfafa hadin gwiwa, musamman ma bisa tsarin shawarar "Ziri Daya da Hanya Daya", da kokarin aiwatar da sakamakon da aka samu a taron dandalin hadin gwiwar Sin da Afirka da ya gudana a birnin Beijing a bara.
Shi kuwa a nasa bangaren, shugaba Al-Bashir na kasar Sudan cewa ya yi, kasarsa na son kara yaukaka zumuncin dake tsakaninta da kasar Sin, da amsa kiran da Sin ta yi, na neman tabbatar da makoma mai kyau ta bai daya ga daukacin bil Adama dake duniyarmu. (Bello Wang)