in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Xi ya aike sakon murnar sabuwar shekarar gargajiya da bikin bazara ga jami'an tsaron Sin
2019-02-03 15:34:44 cri
Shugaban kasar Sin Xi Jinping a jiya Asabar ya aike da sakon taya murnar bikin bazara da na sabuwar shekara bisa kalandar gargajiyar kasar Sin ga sojojin kasar Sin, da rundunar tsaron ta (PLA), da 'yan sanda, sauran masu ayyukan damara na kasar Sin baki daya.

Xi, wanda shi ne babban sakataren kwamitin tsakiyar jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin (CPC), kana shugaban hukumar gudanarwa ta rundunar sojojin kasar Sin (CMC), wanda ya kai ziyara a barikin sojojin na rundunar tsaron PLA dake birnin Beijing, a jajiberin bukukuwan bazara da na sabuwar shekara bisa kalandar gargajiyar kasar Sin, wacca za ta kama a ranar 5 ga watan Fabrairun wannan shekarar.

Da misalin karfe 9:15 na safe, shugaba Xi ya kai ziyara a wajen tsaron tutar kasar Sin dake harabar adana kayan tarihi ta rundunar sojojin kasar ta Sin.

Inda ya bayyana bikin daga tutar kasar Sin a dandanlin Tian'anmen da cewa muhimmin biki ne na kasa baki daya, Xi ya bukace su da su tsaya tsayin daka a bakin aikinsu, domin kare martabar kasar, da kimar tutar kasar Sin, bisa nuna jajurcewa da kishin kasa. (Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China