in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugaban Sin ya aike da sakon taya murnar taron kolin AU karo na 32
2019-02-10 20:42:55 cri

Shugaban kasar Sin Xi Jinping a yau Lahadi ya aike da sakon taya murnar taron kolin kungiyar tarayyar Afrika AU karo na 32 a Addis Ababa na kasar Habasha.

Da yake bayyana kungiyar a matsayin wani dandalin hadin kai da karfafa dangantaka, Xi ya ce a shekarar da ta gabata, shugabancin AU ya samar da muhimman cigaba, inda kasashen na Afrika suke iya yin magana da murya guda game da muhimman batutuwa dake shafar harkokin kasa da kasa da na shiyya kana tasirin kasashen Afrika a harkokin duniya yana cigaba da karuwa.

Kasar Sin a shirye take ta yi aiki da Afrika wajen aiwatar da muhimman kudurorin da aka cimma a taron kolin FOCAC na Beijing, domin gina shawarar ziri daya da hanya daya da aiwatar da ajandar cigaban nahiyar Afrika ta AU nan da shekarar 2063, da kuma ajandar raya cigaban bil adama ta MDD nan shekarar 2030 da sauran muhimman dabarun raya cigaban kasashen Afrika, in ji Xi.

Ta hanyar aiwatar da wannan, bangarorin biyu za su samu damar kara zurfafa mu'amala a tsakanin al'ummomin Sin da Afrika don samar da makoma mai kyau ga bil adama, in ji Xi.(Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China