in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Majalisar ministocin Birtaniya ta goyi bayan yarjejeniyar ficewar kasar daga EU
2018-11-15 10:07:59 cri
Firaministar kasar Birtaniya Theresa May ta bayyana a jiya cewa, majalisar ministocin kasar ta goyi bayan kunshin yarjejeniyar ficewar Birtaniya daga kungiyar EU, wannan wani muhimmin mataki ne game da shirin ficewar kasar daga EU.

Madam May ta bayyana hakan ne bayan kammala taron majalisar ministocin kasar na tsawon awoyi 5. Ta bayyana cewa, ko da yake za a fuskanci matsala da kalubale yayin da Burtaniyar ke kokarin ficewa daga EU, amma ta yi imani cewa, kudurin da majalisar ministocin kasar ta tsaida ya dace da muradun kasar Birtaniya baki daya.

Madam May ta ce, bayan doguwar tattaunawa da ministocin kasar suka yi, sun gani cewa, yarjejeniyar ita ce mafi kyau da Birtaniya da kungiyar EU suka cimma daidaito a kai. A yau ne kuma ake sa ran za ta yiwa majalisar wakilan kasar bayani game da wannan batu.

Kasar Birtaniya da kungiyar EU sun cimma daidaito kan yarjejeniyar ficewar kasar daga kungiyar EU a ranar 13 ga wata. Kafofin watsa labaru na kasar sun yi tsammani cewa, wannan wani babban ci gaba ne da aka samu tun bayan da aka fara yin shawarwari game da wannan batu a cikin shekara fiye da daya. (Zainab)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China