in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Burundi ta yi watsi da rahoton MDD game da matsalar karancin abinci a kasar
2018-02-22 10:23:15 cri
Gwamnatin kasar Burundi ta yi fatali da rahoton da hukumar kula da jin kai ta MDD OCHA ta fitar, inda ta nuna cewa, kimanin 'yan kasar Burundin miliyan 3.6 ne ke fama da matsalar karancin abinci a kasar.

A ranar Litinin ne dai ofishin jin kai na MDDr (OCHA), ya gabatar da wani rahoto game da jadawalin shirin bada agaji na kasar Burundin na shekarar 2018, inda ya nuna cewa, yanayin bukatar tallafin abinci a kasar na kara kamari. Sai dai gwamnatin Burundin ta yi watsi da rahoton, ta bayyana cewa rahoton cike yake da kurairayi da alkaluma na bogi, inji mai magana da yawun shugaban kasar Burundin Philippe Nzobonariba.

Nzobonariba yace, OCHA bata gudanar da aikin hadin gwiwa tare da ma'aikatun gwamnatin kasar ba kamar su ma'aikatar cikin gida, da ma'aikatar kare hakkin dan adam, ma'aikatar lafiya, da ma'aikatar aikin gona a lokacin da take rubuta rahoton.

Ya ce hukumar ta OCHA ta wuce gona da iri, wajen bayyana alkaluman mutanen dake fama da matsalar karancin abinci a kasar, kuma gwamnatin kasar tace ba wannan ne karon farko da ta saba yin hakan ba.

Nzobonariba ya ce, gwamnatin kasar tana cike da mamaki kasancewar yanayin matsalar abinci a kasar a shekarar 2018 ta yi matukar kyautata idan aka kwatanta da shekarar 2017, bisa irin kokarin da ma'aikatun gona da na lafiya suka yi na kwashe mazauna sansanonin 'yan gudun hijirar Burundin an samu sakamako mai kyau.

A cewar rahoton na OCHA, alkaluman data fitar sun nuna cewa, kusan kashi 1 bisa 3 na 'yan kasar Burundin ne ke fama da matsalar karancin abinci. Kuma mata da kananan yara sune matsalar tafi shafa.(Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China