Gobarar da ta tashi a babban ofishin INEC dake Akwa, babban birnin jihar, ta kama kwantainoni biyu dake dauke da na'urorin tantance masu kada kuri'a a zaben da za a yi ranar Asabar.
Kwamishinan INEC na jihar, Nwachukwu Orji da ya tabbatar da tashin gobarar, ya ce jami'an kwana-kwana da na tsaro ne suka yi nasarar kashe gobarar.
A cewar jaridar THISDAY ta kasar, gobarar ta tashi ne a daya daga cikin kwantainonin da ake amfani da su a matsayin ofishin wucin gadi a cikin hedkwatar hukumar dake jihar.
Sai dai jami'an tsaro sun hana 'yan jarida shiga harabar ofishin dan tantance irin asarar da gobarar ta haifar. (Fa'iza Mustapha)