in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An fara aikin rarraba kayayyakin aikin zabe a Najeriya
2019-02-13 09:51:43 cri

Wani jami'in Najeriya ya bayyana a jiya Talata, cewar sojojin saman Najeriya sun fara aikin rarraba kayayyakin aikin zabe a duk fadin kasar a shirye shiryen da ake na babban zaben da za'a gudanar a kasar a ranar Asabar mai zuwa.

Kakakin rundunar sojojin Najeriyar Ibikunle Daramola, shi ne ya bayyana hakan cikin wata sanarwa, inda ya ce aikin jigilar kayayyakin aikin zaben zai gudana ne a dare da rana, za'a kwashi kayayyakin ne daga filin jirgin saman kasa da kasa na Nnamdi Azikwe dake Abuja inda za'a rarraba su zuwa dukkan jihohin kasar.

A ranar Asabar mai zuwa za'a gudanar da zaben shugaban kasa da na 'yan majalisun dokokin Najeriya.(Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China