Shugaban na Najeriya ya bayyana hakan ne a lokacin wata ganawa da yayi da al'umma inda ya nanata alkawarin da ya dauka na cigaba da bunkasa tattalin arzikin kasar, ta hanyar toshe hanyoyin da kudaden gwamnatin kasar ke zurarewa, da kara samar da manyan ayyuka, kana da aiwatar da shirin farfado da tattalin arzikin kasar da na raya cigaban kasa.
Shugaba Buhari ya ce yayi amana cewa, zuba jari a fannin muhimman ayyukan more rayuwa zai kawowa kasar bunkasuwa.
Game da gina kyakkyawar makoma ga kasar kuwa, shugaba Buhari ya ce, gwamnatinsa za ta samar karin hanyoyin kudaden shiga domin bunkasa cigaban tattalin arzikin kasar da inganta tsarin aikin gwamnati ta hanyar tallafawa kamfanoni masu zaman kansu.
Shugaban na Najeriya ya fadawa kungiyar manyan 'yan kasuwa cewa, gwamnatinsa tana iyakar kokarinta wajen habaka tattalin arzikin kasar ta hanyar aiwatar da wasu sabbin shirye shirye da suka hada da shawo kan matsalolin tsaro da yaki da cin hanci da rashawa.(Ahmad Fagam)