Mohamed Fall, ya bayyana hakan ne cikin wata sanarwar da aka fitar a Abuja, fadar mulkin Najeriya, inda ya ce sakamakon wani binciken jin ra'ayin jama'a na shekarar 2016 zuwa 2017, ya nuna raguwar aikata kaciyar mata a sassan Najeriya. Mohamed Fall, wanda shi ne wakilin asusun UNICEF a kasar, ya ce sakamakon ya nuna kaso kusan 18.4 bisa dari na mata dake tsakanin shekaru 15 zuwa 49 ne aka yiwa kaciyar a tsakanin wadannan shekaru, sabanin kaso 27 bisa dari da aka samu a shekarar 2011. (Saminu Hassan)