Wannan ya biyo bayan matakin da kwamitin zartaswa na jam'iyyar (NEC) ta Social Democratic Party (SDP) ta yi ne a Abuja, babban birnin kasar.
A sanarwar da jam'iyyar ta fitar ta ce ta dauki matakin janyewa takarar ne sakamakon takaddama da doguwar shari'ar da ake fafatawa a tsakanin 'yan takarar jam'iyyar dake neman shugabancin kasar wato tsohon ministan yada labarai na Najeriyar Jerry Gana, da tsohon gwamnan jahar Cross River Donald Duke, wadanda suke son jam'iyyar ta SDP ta ba su takarar shugabancin Najeriya. (Ahmad Fagam)