in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Mutane 5 sun mutu a taron gangamin yakin neman zabe a arewa maso gabashin Najeriya
2019-02-08 15:56:31 cri
Dubun dubatar jama'a ne suka taru a lokacin gangamin yakin neman zaben shugaban Najeriya Muhammadu Buhari wanda yake neman wa'adin mulkin kasar a karo na biyu inda mutane 5 suka mutu, wasu da dama suka jikkata a jahar Taraba dake arewa maso gabashin kasar.

Dorcas Philemon, kakakin asibitin kwararru na jahar Taraba, ya tabbatar da mutuwar mutanen biyar ga manema labarai a Jalingo, babban birnin jahar.

Gidajen talabijin da shafukan sadarwa na zamani sun nuna dubban jama'a da suka yi dafifi a babban filin wasa dake Jalingo domin nuna goyon baya ga shugaba Buhari a lokacin da ya halarci jahar don kaddamar da gangamin yakin neman zabensa tare da wasu manyan jiga-jigan 'yan siyasa.

Sai dai shugaba Buhari, ya bayyana damuwa matuka sakamakon hasarar rayukan da aka samu a lokacin gangamin yakin neman zaben inji sanarwar da aka fitar. (Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China