Babbar sakatariyar ma'aikatar Diana Atwine, ta wallafa a shafinta na tweeter cewa, babu bukatar fargaba tun da sakamakon sun nuna babu cutar, tana mai cewa ma'aikatar za ta inganta tsarin sanya ido da bibiyar cutar.
Da farko a jiya Talata, ma'aikatar da hukumar lafiya ta duniya WHO suka killace mutane 13 wadanda suka dauki gawawakin wasu da ake zargin cutar Ebola ta kashe a gabashin Jamhuriyar Demokradiyyar Congo.
Ma'aikatar lafiyar ta kara da cewa, ta tura ayarinta zuwa lardin Tororo dake gabashin Ugandan, domin binne wadanda suka mutu cikin mutunci. (Fa'iza Mustapha)