Hukumar wadda ta bayyana hakan cikin wata sanarwa, ta ce a halin yanzu an yi kiyasin cewa, aikin gina tashar mai karfin Megawatt 183 ya kai kaso 98.5 cikin 100.
Tun a shekarar 2015 ne dai aka fara aikin gina tashar, bayan da kasar Uganda ta samu rancen kudi daga bankin shigi da fici na kasar Sin, a wani mataki na magance matsalar wutar lantarki da kasar ke fuskanta, matsalar da kwararru suka ce tana shafar ci gaban tattalin arzkin kasar.(Ibrahim)