in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
MDD ta bukaci Uganda ta hada hannu da AU game da kawar da 'yan tawayen Jamhuriyar Demokradiyyar Congo
2018-12-05 10:10:02 cri
Manzon musamman na MDD a yankin manyan Tafkunan Afrika Said Djinnit, ya bukaci Uganda ta hada hannu da Tarayyar Afrika AU da sauran kungiyoyin yankunan nahiyar, a kokarin kawar da 'yan tawaye a gabashin Jamhuriyar Demokradiyyar Congo.

Wata sanarwa daga ma'aikatar harkokin wajen Uganda, ta ce Said Djinnit ya bayyana haka ne a jiya, yayin ganawarsa da ministan harkokin wajen kasar Sam Kutesa.

Said Djinnit, ya ce ya kamata AU da kungiyoyi irinsu ta kasashen yankin manyan tafkunan Afrika da ta raya kasashen kudancin Afrika, da su hada hannu su samar da mafita da za ta fatattaki 'yan tawayen ADF tare da tasa keyar mayakan M23.

Sam Kutesa ya ce Uganda za ta bada goyon baya ga hadin gwiwar, sai dai ya yi kira da MDD ta tsara yadda za a aiwatar da matakin hada kan sauran kasashe ta yadda za a yi hadin gwiwar.

Jami'an biyu sun kuma amince da kawar da 'yan tawayen ya zuwa watan Fabrerun sabuwar shekara.

Taron na zuwa ne bayan wanda aka yi tsakanin Uganda da Jamhuriyar Demokradiyyar Congo, da nufin samar da rundunar kawance don yaki da 'yan tawayen ADF dake gabashin kasar. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China