in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Adadin wadanda suka mutu sanadiyyar hatsarin kwale kwale a Uganda ya karu zuwa 35
2018-11-26 10:10:18 cri

Rundunar sojin Uganda ta ce adadin wadanda suka mutu sanadiyyar hatsarin kwale-kwale a tafkin Victoria a karshen makon da ya gabata, ya karu zuwa 35.

Mataimakin kakakin rundunar Lt. Col Deo Akiiki, ya shaidawa kamfanin dillancin labarai na Xinhua ta wayar tarho cewa, za a ci gaba da aikin bincike da ceto, amma abu ne mawuyaci a samu wadanda ke raye, la'akari da cewa kwale-kwalen ya kife ne ranar Asabar da daddare.

Ya ce ba sa tunanin akwai sauran wadanda ke raye, domin an ceto mutum na karshe dake raye ne tun a daren da lamarin ya auku.

Ya kara da cewa, za su ci gaba da aikin bincike har sai an ba su umarnin dakatarwa, kuma ya yi ammana za su shafe tsawon mako guda ko ma fiye.

Kwale-kwale biyu ne suka nitse cikin ruwa a tsibirin Mutima a ranar Asabar da dare, lamarin da 'yan sanda suka alakanta da daukar mutane fiye da kima da rashin kyan yanayi.

Kwale kwalen na biyu ya nitse ne lokacin da yake aikin ceton kwale kwale na farko da ya nitse, wanda ake liyafa cikinsa.

A cewar 'yan sandan kasar, kawo yanzu, mutane 27 aka ceto. Rahotannin daga kafafen yada labarai sun ruwaito cewa mutane 120 ne suke liyafa a cikin kwlae kwalen lokacin da hatsarin ya auku.

A jiya Lahadi ne gwamnatin kasar ta kafa kwamitin da zai yi bincike kan lamarin, karkashin Firaministan Ruhakana Rugunda. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China