in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
A kalla mutane 10 sun rasu sakamakon nitsewar jirgin ruwa a Uganda
2018-11-25 16:20:13 cri
Rundunar 'yan sandan kasar Uganda ta tabbatar da nitsewar wani jirgin ruwa a tabkin Victoria na yankin Mukono dake tsakiyar kasar, inda ta ce an ceto mutane sama da 40, yayin da mutane 10 suka rasa rayukansu.

Rahoton da rundunar 'yan sandan kasar ta wallafa jiya a shafin intanet, ya ce, ana ci gaba da aikin ceto a yankin, sa'an nan, za a gabatar da karin bayani kan batun.

Ya zuwa yanzu, ba a tabbatar da yawan mutanen dake cikin jirgin ruwan a lokacin da hadarin ya auku ba.

Jiragen ruwan Uganda su kan nitse sakamakon daukan mutane fiye da kima da kuma sauran wasu dalilai. Ko a ranar 22 ga watan Maris din shekarar 2014, nitsewar jirgin ruwa a tabkin Albert dake yammacin kasar, ya yi sanadin mutuwar mutane a kalla 108. (Maryam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China