in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Yan Najeriya fiye da miliyan 84 ne suka yi rijistar kada kuri'a a babban zaben kasar dake tafe
2019-01-08 08:55:05 cri

Shugaban hukumar zabe mai zaman kanta a Najeriya Mahmood Yakubu ya bayyana cewa, sama da 'yan kasar miliyan 84 ne suka yi rijistar kada kuri'a a manyan zabukan kasar da za a gudanar a wannan shekara.

Shugaban wanda ya bayyana hakan ga wakilan jam'iyyun siyasun kasar a Abuja, fadar mulkin kasar, ya ce yanzu haka hukumarsa ta yi rijistar wadanda suka cancaci kada kuri'a miliyan 84,004,084. Kimanin kaso 42 cikin 100 na yawan al'ummar kasar miliyan 198. Adadin da ya kai kimanin mutane 15.2 fiye da adadin 'yan Najeriya miliyan 68.8 da suka kada kuri'a a zabukan kasar na shekarar 2015.

A watan Agusta ma hukumar ta tabbatar da cewa, jam'iyyun siyasu 91 ne suka yi rijistar fafatawa a manyan zabukan kasar. Daga cikin wannan adadi, 'yan takara 73 ne za su tsaya neman shugabancin kasar a zaben na watan Fabrairu.(Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China