in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Tsohon mataimakin shugaban Najeriya ya bayyana aniyarsa ta tsayawa takarar shugabancin kasar
2018-07-23 09:53:06 cri

Tsohon mataimakin shugaban Najeriya Atiku Abubakar, ya sanar da aniyarsa ta tsayawa takarar a zaben shugaban kasar na shekarar 2019 karkashin inuwar jam'iyyar adawa ta PDP a hukumance.

A ranar Asabar ce dai Atiku Abubakar, wanda ya rike mukamin mataimakin shugaban kasar daga shekarar 1999 zuwa 2007, ya sanar da aniyarsa ta neman kujerar shugabancin kasar yayin wani gangami da ya shirya a garin Yolan jihar Adamawa dake yankin arewa maso gabashin kasar.

Da yake jawabi Atiku ya shaidawa magoya bayansa cewa, zai yi duk mai yiwuwa na ganin jihar Adamawa wadda da ma jihar PDP ce ta koma karkashin jam'iyyar PDP a shekarar 2019.

Ya ce jam'iyyar APC mai mulki ta gaza a fannonin tattalin arziki, tsaro da samar da ayyukan yi, kuma idan har aka zabe shi, zai magance wadannan matsaloli da ya ce APCn ta gaza aiwatar da su.

A nasa jawabin shugaban jam'iyyar adawa ta PDP Uche Secondus, ya bayyana Atiku a matsayin dan takarar da yake da dukkan abubuwan da ake bukata, wanda zai iya kayar da APC a zaben shekarar 2019.

Secondus ya kuma baiwa dukkan 'yan takarar shugabancin kasar karkashin laimar PDP tabbacin yiwa kowa adalci. Ya kuma bukaci APC da ita ma ta yiwa dukkan jam'iyyun adalci a zaben na shekarar 2019. (Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China