in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugaba Buhari na Najeriya ya kaddamar da yakin neman zaben shugaban kasa na 2019
2018-12-29 15:50:54 cri
A jiya Juma'a shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya kaddamar da gangamin yakin neman zaben shugaban kasar, zaben da za'a gudanar a watan Fabrairun shekara mai zuwa.

Shugaba Buhari, wanda a kwanan baya babbar jam'iyyar adawar kasar ta zarge shi da rashin mayar da hankali kan batun yakin neman sake zabarsa a shugabancin kasar, sai dai a ranar Juma'a shugaban ya kaddamar da yakin neman zaben nasa a Uyo, babban birnin jahar Akwa-Ibom, dake shiyyar kudu maso kudancin kasar.

Da yake yiwa dandazon magoya bayansa jawabi a filin taron gangamin yace, ya cika alkawurran da ya daukawa 'yan kasar a lokacin yakin neman zabensa a shekarar 2015, duk kuwa da irin shakkun da bangaren 'yan adawar kasar suke nunawa game da ikirarin shugaban.

Yace idan aka sake zabarsa a karo na biyu, zai tabbatar da magance barazanar mayakan kungiyar 'yan ta'adda na Boko Haram a fadin kasar.

Ya kara da cewa, batun rashin aikin yi ya kasancewa wani babban kalubale a kasar, shugaba Buhari ya ce, gwamnatin tana yin iyakar kokarinta wajen magance matsalar.

Shugaban na Najeriya yace, gwamnatinsa zata cigaba da yaki da rashawa idan aka zabe shi a karo na biyu a zaben shekarar 2019.

A farkon wannan makon ne, Buhari ya ce zai kaddamar da babban gangamin yakin neman zabensa na neman wa'adin mulki karo na biyu.

Yace manyan batutuwan yakin neman zaben jam'iyyar APC mai mulki guda 3 da suka hada da batun bunkasa tattalin arziki, tabbatar da tsaro da kuma yaki da rashawa.

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China