in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugaban Najeriya ya kaddamar da yakin neman zabensa a yankin arewa maso gabashin kasar
2019-01-22 09:28:53 cri

A jiya ne shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya ziyarci jihohin Borno da Yobe dake yankin arewa maso gabashin kasar,inda ya nemi goyon bayan masu jefa kuri'a yayin manyan zabukan kasar da za su gudana a wata mai zuwa.

Shugaba Buhari ya jagoranci manyan jagororin jam'iyyar APC mai mulki zuwa garin Maiduguri,fadar mulkin jijhar Borno da kungiyar Boko Haram ta yi kaurin suna da kuma garin Damaturu,fadar mulkin jihar Yobe da nufin karfafawa masu zabe gwiwar su marawa jam'iyyarsa da ma 'yan takararta baya a zabukan dake tafe.

Yayin da yake garin Maidugiri, shugaba Buhari ya yi alkawarin cewa, idan har aka sake zabarsa, zai bullo da managartan dabarun tsaro da ma shirye-shiryen farfado da tattalin arziki domin magance kalubalen rayuwa da tattalin arzikin dake addabar kasar.

Shugaba Buhari ya kuma yi alkawarin yakar matsalar cin hanci da rashawa yadda ya kamata.

Yankin arewa maso gabashin kasar dai, shi ne bangaren kasar da rikicin Boko Haram ya fi shafa. Dakarun tsaro sun fi mayar da hankali ne kan ayyukan kungiyar a jihohin Adamawa da Borno da Yobe.

A baya-bayan nan ma,kungiyar Boko Haram ta kaddamar da jerin hare-hare a yankin arewa maso gabashin Najeriyar, inda ta kafa tutocinta a garuruwa da dama har ma ta kwace sansanin sojojin kasashen dake yaki da mayakan kungiyar.(Ibahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China