in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugaban Najeriya ya yi alkawarin gudanar da zabe cikin adalci
2019-01-08 09:16:42 cri

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya bayyana kudurinsa na ganin an gudanar da zabukan kasar a wata mai kamawa cikin adalci wadda kowa zai amince da shi.

Shugaba Buhari ya bayyana hakan ne yayin da yake jawabi a taron gangamin siyasa da jam'iyyar APC mai mulkin kasar ta shirya a Abuja, babbar birnin kasar. Ya ce, shirya zabe mai tsafta da kowa zai yi na'am da shi, shi ne ginshikin dorewar siyasa da wanzuwar zaman lafiyar kasa.

Shugaba Buhari, ya kuma nanata kudurinsa na ganin ya bar tsarin demokiradiyar da kowa zai yi na'am da shi. Za kuma a cimma wannan nasara ce kadai ta hanyar shirya zaben gaskiya da adalci.

Buhari ya ce, tun daga shekakar 2015, tsarin zabukan kasar mafi yawan al'umma a nahiyar Afirka ke ci gaba da inganta. Wannan ya sa, a cewar shugaba Buhari, suka nace cewa, wajibi ne a kidaya kuri'u, kana gwamnati ta daina tsoma baki a harkokin da suka shafi zabuka.

Daga shekarar 2015 zuwa yanzu hukumar zaben kasar mai zaman kanta (INEC) ta shirya zabuka masu tsafta a mazabu 195 na fadin kasar, wadanda kuma aka yi imanin cewa, sun fi zabukan da suka gabata inganci.

Shugaba Buhari dai zai sake tsayawa takara a zabukan kasar da zai gudana a ranar 16 ga watan Fabrairu don neman wa'adin mulki na biyu, duk da shakkun da wasu ke nunawa kan lafiyar shugaban mai shekaru sama da 76 da jan ragamar kasar mafi karfin tattalin arziki a nahiyar.(Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China