Abdel Fattah al-Sisi, wanda ya karbi shugabancin kungiyar na karba karba na tsawon shekara 1, daga shugaban Rwanda Paul Kagame, ya ce cikin shekara 1 mai zuwa, zai yi aiki tukuru wajen cimma muradun da AU ta fitar yayin taron, wadanda suka hada da fara aikin yankin ciniki cikin 'yanci na nahiyar da tsugunar da 'yan gudun hijira da kuma samar da aikin yi ga dimbin matasan nahiyar.
AU ta bayyana a ranar Juma'ar da ta gabata cewa, rikice-rikice daban daban a fadin nahiyar Afrika, sun raba mutane miliyan 20.8 da matsugunansu.
A cewar shugaba Al-Sisi, taron na AU karo na 32 mai take kan 'yan gudun hijira, ya bayyana yadda daidaitar jama'a ka iya haifar da kalubalen zamanta kewa da siyasa da tsaro da tattalin arziki a nahiyar, a don haka, zai mayar da hankali kan bangaren a cikin shekara 1 mai zuwa. (Fa'iza Mustapha)