in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Jami'an Afirka sun yaba alakar dake tsakanin Sin da Afirka
2019-02-11 20:32:33 cri

Jami'an kasashen Afirka sun yaba alaka da hadin gwiwar dake tsakanin Sin da Afirka a fannoni daban-daban, karkashin jagorancin shugaba Xi Jinping na kasar Sin, wanda ya aike da sakon taya murna ga taron kolin kungiyar AU karo na 32 da aka bude a birnin Addis Ababan kasar Habasha.

Babban sakataren hukumar aikewa da wasiku ta kungiyar AU Younouss Djibrine, ya shaidawa kamfanin dillancin labarai na Xinhua cewa, shugabannin kasashen Afirka suna kara ganawa da shugaban kasar Sin don kara zurfafa alakar moriyar juna dake tsakanin bangarorin biyu wato Sin da Afirka.

Djibirine ya ce, alakar dake tsakanin Sin da Afirka karkashin shawarar ziri daya da hanya daya, wadda ta mayar da hankali kan bunkasa kayayyakin more rayuwa da hade sassan biyu, wani shiri ne na gwaji kan raya Afirka da kulla alaka a sauran fannoni, musamman aikewa da wasiku da ayyukan ba da hidima.(Ibrahim Yaya)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China