A jawabinsa na bude taron, shugaban kwamitin gudanarwar AU, Moussa Faki Mahamat, ya ce batun tilastawa jama'a kauracewa muhallansu na daya daga cikin abubuwan dake tayar da hankali a kasashen na Afrika.
"Abu mai muhimmanci shi ne a kara daukar matakai na shawo kan matsalar tun daga tushe, ta hanyar ayyukan hukumomin tallafawa rayuwar bil adama na Afrika," in ji Mahamat.
A lokacin bude taron, shugaban kasar Masar Abdel-Fattah al-Sisi ya karbi shugabancin taron kolin daga wajen Paul Kagame shugaban kasar Rwanda.
Da yake jawabi a lokacin taron, al-Sisi ya bukaci a kara kokari wajen bunkasa zaman lafiya da tsaro da tallafawa 'yan gudun hijira, bakin haure, da kuma mutanen dake rayuwar a sansanonin da aka kebewa mutanen da rikici ya tilastawa ficewa daga muhallansu.
Haka zalika ya jaddada bukatar a kara kaimi wajen yaki da ta'addanci da masu tsattsauran ra'ayin addini da kuma bunkasa muhimman kayayyakin more rayuwa da raya birane a nahiyar baki daya. (Ahmad Fagam)