in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An bude taron kolin AU karo na 32 a babban birnin kasar Habasha
2019-02-10 20:45:20 cri

A yau Lahadi aka bude taron kolin kungiyar tarayyar Afrika (AU) karo na 32 a hedkwatar kungiyar tarayyar Afrikan dake Addis Ababa.

Taken taron na kwanaki biyu na shekarar 2019 shi ne, "Sake komawar 'yan gudun hijira gidajensu, da mutanen dake rayuwa a sansanonin mutanen da rikici ya raba da gidajensu: Domin samar da hanya mai dorewa don magance raba jama'a da gidajensu a Afrika."

Batun tilastawa mutane barin gidajensu da 'yan gudun hijira a Afrika da kuma sauye sauye ga kungiyar ta AU, da zaman lafiya da tsaro suna daga cikin muhimman batutuwan da suka mamaye taron kolin AU na bana.

A jawabinsa na bude taron, shugaban kwamitin gudanarwar AU, Moussa Faki Mahamat, ya bukaci a rubanya kokari wajen sake yin gini kan irin nasarorin da aka cimma a bangarori daban daban, ciki har da batun ciniki cikin 'yanci a tsakanin nahiyar, da zaman lafiya da tsaro, da yin sauye sauye ga hukumomin harkokin kudi na kungiyar.(Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China